Kofin FA: Liverpool ta doke Plymouth 1-0

Lucas Leiva na murnar kwallon da ya ci

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ba ko da daya daga cikin 'yan wasan Liverpool na yanzu da ke kungiyar lokacin da Lucas Leiva ya ci kwallonsa ta karshe a 2010

Lucas Leiva ya ci kwallonsa ta farko a Liverpool cikin shekara 7, wadda ta ba su damar zuwa zagaye na hudu na gasar cin kofin FA a karawarsu da kungiyar Plymouth da ke gasar League Two.

Liverpool ta yi tafiyar nisan mil 293 zuwa gidan kungiyar ta Plymouth ta gasar League Two ta Ingila, bayan haduwar farko da suka yi wadda suka tashi canjaras ba ci, a Anfield.

Lucas ya ci kwallon ne a minti 18 da fara wasa da ka, bayan da Philippe Coutinho ya dauko wani bugun kusurwa (kwana).

A wasan Divock Origi ya barar da bugun fanareti, wanda mai tsaron ragar masu masukin bakin Luke McCormick ya kama.

Lucas dan Brazil yana Liverpool tun 2007, amma ba ya cin kwallo sosai a wasa. Kwallon da dan wasan na tsakiya ya ci, ita ce ta farko tun lokacin da suka doke Steaua Bucharest 4-1 a gasar Europa, a watan Satumba na 2010.

Plymouth, wadda take mataki 66 kasa da Liverpool a jerin kungiyoyin da suka iya kwallo ta kusa farke kwallon lokacin da Jake Jervis ya doki wata kwallo da birkice, ta bugi sandar raga, bayan minti 20 da dawowa daga hutun rabin lokaci.

Sakamakon nasarar Liverpool za ta hadu a gidanta da kungiyar Wolverhampton Wanderers ranar 28 ga watan Janairu.