Man United: Rooney ya kafa tarihin zura kwallaye

Asalin hoton, Getty Images
Wayne Roony ya zurawa Man United kwallaye 250 jumulla
Dan wasan gaba na Manchester United Wayne Rooney ya kafa tarihin zama wanda yafi kowa ci wa kulob din kwallaye, bayan da ya zura kwallo daya a wasan da United din ta tashi 1-1 da Stoke City a gasar Premier.
Rooney ya farkewa United kwallo daya da aka zura mata ne ta bugun tazara, abin da ya sa jumullar kwallayen da ya ci wa kulob din suka kai 250.
Da wannan kwallo da ya ci, Rooney ya shiga gaban Sir Bobby Charlton wanda ya ci wa United kwallaye 249 jumulla.
Kafin Manchester United ta farke kwallo dayan, Stoke City ta yi yunkurin lashe wasanni uku a jere ne a gasar ta Premier.
Har yanzu dai Manchester United din ta na mataki na shida ne a teburin Premier, inda maki uku ne kadai tsakaninta da Arsenal wacce ke mataki na hudu.
Hakazalika kuma tazarar maki 11 ne tsakaninta da Chelsea wacce ke mataki na daya.