Da kyar Arsenal ta kwaci kanta a hannun Burnley

Gasar cin kofin Premier mako na22
Bayanan hoto,

Fenaritin da Alexis Sanchez ya ci wadda ta bai wa Arsenal damar hada maki uku a gasar mako na 22 a gasar ta Premier

Arsenal ta hada maki uku a kan Burnley a wasan mako na 22 a gasar cin kofin Premier da suka kara a ranar Lahadi a Emirates.

Arsenal mai masaukin baki ce ta fara cin kwallo ta hannun Shkodran Mustafi, kafin daga baya a farke ta hannun Andre Gray a bugun fenariti, bayan da Francis Coquelin ya yi wa Ashley Barnes keta a da'ira ta 18.

Daf da za a tashi daga karawar alkalin wasa Jon Moss ya samu Ben Mee da laifin kai da kafa tsakaninsa da Laurent Koscielny a da'ira ta 18 ta Burnley, hakan ya sa aka bai wa Arsenal bugun fenariti.

Alexis Sanchez ne ya buga fenaritin ta kuma fada raga wanda hakan ne ya sa Gunners ta ci wasannin Premier biyar a gida a jere, kuma Arsenal din ta koma ta biyu a kan teburin gasar da maki 47.

Arsenal ta kammala fafatawar da 'yan kwallo 10 a cikin fili, bayan da aka bai wa Granit Xhaka jan kati saura minti 25 alkalin wasa ya busa tashi.