Barcelona ta ci gaba da zama ta uku a La Liga

Gasar cin kofin La Liga Spaniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Barcelona tana nan a matakinta na uku a kan teburin La Liga

Barcelona ta samu nasarar doke Eibar da ci 4-0 a gasar La Liga wasan mako na 19 da suka fafata a ranar Lahadi.

Barcelona wadda ta ziyarci Eibar, ta fara cin kwallo ta hannun Denis Suarez saura minti 14 a je hutun rabin lokaci.

Bayan da aka dawo ne daga hutun Lionel Messi ya ci ta biyu, sai Luis Suarez da ya kara ta uku da kuma Neymar wanda ya ci ta hudu daf da za a tashi daga karawar.

Da wannan sakamakon Barcelona tana mataki na uku a kan teburin da maki 41, Seville ce ta biyu da maki 42.

Real Madrid ce ke matsayi na daya a kan teburin da maki 43, kuma tana da kwantan wasa daya.