Chelsea ta bai wa Arsenal tazarar maki takwas

Asalin hoton, PA
Diego Costa ya ci kwallaye 15 a gasar Premier bana
Chelsea ta ci gaba da jan ragamar teburin Premier, bayan da ta doke Hull City 2-0 a gasar cin kofin Premier wasan mako na 22 da suka fafata a Stamford Bridge.
Chelsea ta ci kwallon farko ta hannun Diego Costa wanda ya ci ta 15 jumulla a gasar bana, ya kuma yi kan-kan-kan da Alexis Sanchez na Arsenal a yawan zura kwallaye a raga a wasannin da ake yi.
Costa bai buga karawar da Chelsea ta doke Leicester City a gasar Premier a ranar Asabar da ta wuce ba, inda koci Conte ya ce dan kwallon na fama da ciwon baya ne.
Sai dai kuma a makon da ya wuce din aka yi ta rade-radin cewar dan wasan na Spaniya zai koma China da murza-leda ne.
Mai tsaron baya Garry Cahill ne ya ci ta biyu saura minti tara a tashi daga gumurzun, wanda hakan ya bai wa Chelsea maki uku a wasan.
Da wannan sakamakon Chelsea tana mataki na daya a kan teburin Premier da maki 55, yayin da Arsenal wadda ta ci Burnley a ranar Lahadi ta koma ta biyu da maki 47.
Chelsea za ta karbi bakuncin Brentford a gasar cin kofin FA wasannin zagaye na hudu a ranar Asabar.