Ronaldo ya yi wasanni 250 a gasar La Liga

Asalin hoton, Getty Images
Ronaldo ya koma Madrid a 2009 ya kuma ci kwallaye 273 a gasar La Liga
Cristiano Ronaldo ya buga wa Real Madrid wasa na 250 a Gasar cin Kofin La Liga ranar Asabar, a karawar da Real Madrid ta doke Malaga 2-1--daya daga cikin wasannin mako na 19.
Dan wasan, wanda kuma shi ne kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Portugal, ya koma Spaniya da taka leda ne a 2009.
Ronaldo ya fara buga wa Madrid wasa a ranar 29 ga watan Agustan 2009, a fafatawar da Real ta ci Deportivo 3-2, kuma yana cikin 'yan wasan da suka ci kwallaye.
Dan wasan ya ci wa Real Madrid kwallo 273, inda ya ci 153 a Bernabéu, sannan ya zura 120 a wasannin da ya buga a waje.
Daga cikin wasa 250 da Ronaldo ya buga a La Liga, Real ta ci 190, sannan ta yi canjaras a karawa 34; aka kuma doke ta a fafatawa 26.
A kakar wasa ta 2011/12 ne Ronaldo ya yi wa Real Madrid dukkan wasannin gasar La Liga 38 da aka buga, a kuma shekarar ce ya lashe Kofin Gasar.
Bayan da ya yi wasa 250 a Gasar La Liga, Ronaldo ya karbi kyautar takalmin zinare uku a matsayin wanda ya fi cin kwallo a gasar.