Odey ya fara cin kwallaye uku a gasar Nigeria

Gasar cin kofin Nigeria

Asalin hoton, LMCNPFL Twitter

Bayanan hoto,

Odey ne ya fara cin kwallaye uku a gasar Firimiyar Nigeria

Dan wasan Mountain of Fire, Stephen Odey, ya zama na farko da ya ci kwallaye uku rigis a gasar Firimiyar Nigeria ta bana.

Odey ya samu nasarar cin kwallayen ne a wasan mako na uku a gasar, bayan da kungiyarsa ta ci Lobi Stars 4-0 a Legas a ranar Lahadi.

Ita kanta MFM ta kwashi kwallaye 4-0 a hannun Ifeanyi Ubah a wasan mako na biyu da suka fafata a ranar Laraba, saboda haka ta huce a kan Lobi Stars.

A wasannin mako na ukun da aka yi a ranar Lahadin, an ci kwallaye 19 a raga, kuma babu wasan da aka yi canjaras, babu kuma kungiyar waje da ta ci wasa.

A ranar Laraba za a ci gaba da wasannin mako na hudu a gasar ta Firimiyar Nigeria, inda Shooting Stars wadda ta yi rashin nasara a hannun Pillars da ci 2-1 za ta karbi bakuncin MFM.