An tuhumi Arsene Wenger da rashin da'a

Gasar cin kofin Premier

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Wenger ya nemi afuwa kan halin da ya nuna a lokacin wasan

An tuhumi kociyan Arsenal, Arsene Wenger, da nuna halin rashin da'a yayin wasan da kungiyarsa ta buga ranar Asabar a Emirates da Burnley, wanda ta lashe da ci biyu da daya, a gasar Premier.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila, FA, ta tuhumi kociyan da ture alkalin wasa mai jiran kar-ta-kwana da kuma fada wa alkalin wasan munanan kalamai.

An kori Wenger a wasan a lokacin da ya yi fushi saboda bai wa Burnley fenariti da aka saura minti bakwai a tashi daga karawar, a lokacin Arsenal ta ci kwallo daya.

Bayan da aka kammala wasan, Wenger ya nemi afuwa.

Hukumar ta bai wa kociyan na Arsenal zuwa ranar Alhamis da yammaci domin ya kare kansa.