Sergio Busquets na Barcelona zai yi jinya

Gasar cin kofin La Liga na Spaniya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Barcelona tana mataki na uku a kan teburin La Liga

Sergio Busquets zai yi jinya, bayan raunin da ya yi a karawar da Barcelona ta ci Eibar 4-0 a wasan La Liga da suka fafata a ranar Lahadi.

Dan kwallon mai shekara 28, ya yi rauni ne a minti na takwas da fara wasan, bayan da Nicolas Escalante na Eibar ya yi masa keta.

Barcelona ba ta sanar da lokacin da Busquets wanda ya buga mata wasanni 27 daga 32 da ta yi a kakar bana, lokacin da zai dawo fagen tamaula ba.

Tun farko Barcelona ta yi rashin Andres Iniesta wanda shi ma ke yin jinya.

Barcelona za ta karbi bakuncin Real Sociedad a ranar Alhamis a wasa na biyu a gasar Copa del Rey karawar daf da na kusa da karshe.

Barca ce ta samu nasara da ci daya mai ban haushi a gidan Sociedad a wasan farko da suka yi.