Real Madrid za ta ziyarci Celta a Copa del Rey

Gasar cin Copa del Rey

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Celta ce ta ci Madrid 2-1 a wasan farko da suka kara a Benerbeu

Celta de Vigo za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasa na biyu na daf da na kusa da karshe a gasar Copa del Rey a ranar Laraba.

A karawar farko da kungiyoyin biyu suka buga a Bernebeu Celta ce ta ci Real Madrid 2-1.

Iago Aspas ne ya fara ci wa Celta kwallo a minti na 64 a wasan, daga baya ne ne Madrid ta farke ta hannun Marcelo Vieira Da Silva, Celta ta kara cin kwallo na biyu ta hannun Jonny.

Bayan nan SD Eibar za ta fafata da Atletico de Madrid a ranar Laraba, a wasan farko da suka kara Atletico ce ta samu nasara da ci 3-0.

Barcelona wadda ta ci Real Sociedad1-0 a wasan farko, za ta karbi bakuncin wasa na biyu a ranar Alhamis.