An zargi Xhaka da furta kalaman wariya

Gasar cin kofin Premier

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

An bai wa Xhaka jan kati a ranar Asabar a wasan da Arsenal ta ci Burnley 2-1

'Yan sanda sun yi wa dan kwallon Arsenal, Granit Xhaka, tambayoyi a kan zargin da ake yi cewa ya furta kalaman wariya ga wani ma'aikacin filin jirgin sama a daren Litinin.

Lamarin ya faru ne a lokacin da Xhaka mai shekaru 24 ya raka wani abokinsa filin jirgin sama na Heathrow domin komawa gida, bayan da ya kai masa ziyara.

Abokin Xhaka ya je filin jirgin a makare a dalilin haka aka hana shi shiga jirgin da ya kamata ya kai shi Jamus, a lokacin ne dan kwallon na Arsenal ya furta kalaman.

Kungiyar Arsenal ba ta ce komai ba a kan lamarin, tana mai cewa batu ne da bai shafi tamaula ba, kuma 'yan sanda na yin bincike babu abin da za ta ce.

Takaddamar ta faru ne kwana daya da bai wa Xhaka jan kati a karawar da Arsenal ta ci Burnley 2-1 a gasar Premier.