Ferguson ya yaba wa Mourinho

Gasar Premier ta Ingila

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester United tana mataki na shida a kan teburin Premier

Tsohon kociyan Manchester United, Sir Alex Ferguson ya ce Jose Mourinho na samun ci gaba kan yadda yake jan ragamar United, kuma rashin sa a ne da bai kalubalanci Chelsea ba.

A hira da Ferguson ya yi da BBC ya ce Mourinho yana gudanar da aikinsa kamar yadda ya kamata, bayan da kungiyar ke mataki na shida a kan teburin Premier bana.

Tsohon kocin na United ya ce Mourinho ya yi canjaras a wasanni shida, ban da hakan da yanzu United tana kafada da kafada da Chelsea.

Ferguson ya yi ritaya a 2013, amma ya ci gaba da halartar wasu wasannin da United ke yi gida da waje.

Jose Mourinho ya karbi aikin jan ragamar Manchester United a matsayin koci na uku a watan Mayu, inda ya maye gurbin Louis van Gaal tun bayan da Ferguson ya yi ritaya.