An kwace lambar zinariya ta Usain Bolt

Gasar wasannin Olympic

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Carter aka samu da laifin shan abu mai kara kuzarin wasa a 'yan wasan Jamaica

Kwamitin wasannin Olympic na duniya ya kwace lambar zinariya ta Nesta Carter dan kasar Jamaica, sakamakon samunsa da laifin shan abubuwa masu kara kuzari.

Nesta ya wakilci Jamaica a tseren mita 100 ta 'yan wasa hudu a gasar Olympic da aka yi a shekarar 2008, kuma kasar ce ta lashe tseren.

Sakamakon hakan ne yasa aka kwace lambar zinare guda hudun da 'yan wasan Jamaica suka ci a tseren mita 100 da aka yi a Beijing, cikinsu har da ta Usain Bolt.

Hakan kuma na nufin Bolt din ba shi ne dan wasa na farko da ya lashe lambobin zinare uku a jere a wasannin kakar Olympic uku ba.

Kwamitin na Olympic ya ce ya samu Carter da laifin yin amfani da Methylhexaneamine, wanda daya ne daga cikin abubuwan da aka haramta a jerin kayayyakin da suke kara kuzari a wajen wasanni.