Filippe Coutincho ya saka hannu kan sabuwar yarjejeniya ci gaba da wasa a Liverpool

Philippe Coutinho

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tsawaita Kontiragin Philippe Coutinho ya nuna farin cikinsa da zama a Liverpool

Filippe Coutinho, ya saka hannu a sabuwar yarjejeniya da Liverpool, inda zai ci gaba da buga mata tamaula har tsawon shekara biyar.

kwantiragin da ya rattaba hannu ya sa ya zama dan kwallon kungiyar da ya fi karbar albashi mai tsoka, wanda zai dunga karbar fam 150,000 a duk mako.

Dan wasan Brazil din mai shekara 24 ya koma Liverpool ne daga Inter Milan kan kudi fam miliyan 8.5 a watan Janairun 2013, kuma sabuwar yarjejeniyarsa za ta kaishi shekarar 2022.

Coutinho ya ci kwallaye 34 a wasanni 163 da ya buga wa Liverpool tun lokacin da ya koma can da murza-leda..

Dan wasan ya shaida wa shafin internet na Liverpool cewar "Kungiya ce wadda nake matukar godewa, kuma wannan ya nuna farin ciki na a nan".

Liverpool za ta kara da Southampton a wasa na biyu a gasar League Cup a Anfield, wasan farko Southampton ce ta ci Liverpool daya mai ban haushi.