An haramta wa wani mai goyon bayan Bastia zuwa filin wasa, bayan da aka same shi da laifin fada wa Mario Balotelli batanci

Mario Balotelli

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mario Balotelli ya ci kwallaye 10 wa kungiyar Nice a wasanni 15 a kakar bana

An haramta wa wani mai goyon bayan kungiyar Bastia zuwa kallon wasanninta, bayan da aka same shi da laifin fada wa dan wasan Nice Mario Balotelli kalamun batanci.

Kungiyar kwallon kafa ta Bastia ce ta haramta wa mutumin wanda ba ta bayyana sunansa ba zuwa kallo a filin wasanta, bayan da ya aikata laifin a karawar da suka tashi babu ci da Nice a ranar Juma'a.

Balotelli, Tsohon dan kwallon Liverpool da Machester City, mai shekara 26, ya wallafa a shafukan sada zumunta cewar an yi ta cin zarafinsa da kiransa biri a wasan da suka yi a ranar juma'a.

Kungiyar Bastia ta ce "wani mutum mai kimanin shekara 40" yagabatar da kansa a gaban kwamitin da hukumar gudanar da gasar cin kofin Faransa ta kafa da cewar shi ne ya aikata laifin.

Balotelli ya ci wa kungiyar Nice kwallaye 10 a wasanni 15 da ya buga mata, tun bayan da ya koma can daga Liverpool a watan Agustan da ya wuce.