Masar ta samu zuwa mataki na gaba a gasar cin kofin Afirka bayan ta ci Ghana 1-0.

Muhamed Salah

Asalin hoton, Justin Talis

Bayanan hoto,

'Yan tawagar Masar sun kewaye Mohamed Salah bayan ya ci kwallon da ya raba gardama a wasan

Masar ta zama daya daga cikin kasashe takwas da suka samu zuwa matakin daf da na kusa da na karshe a kofin Afirka bayan ta doke Ghana 1-0.

Muhammad Salah ne ya ci kwallon a bugun tazara, wanda hakan ya bai wa Masar damar kai wa zagayen gaba, ta kuma jagoranci rukuni na hudu.

Wani kuskure daga golan Ghana, Brimah Razak, ya baiwa Marwan Mohsen damar kara cin kwallo na biyu, amma da ya buga ta sai ta yi sama.

Shi ma Daniel Amartey ya barar da damar da Ghana ta samu mafi kyau.

Da wannan sakamakon Masar za ta kara da Morocco a wasanin daf da na kusa da na karshe, ita kuwa Ghana za ta kece raini da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.