Barcelona za ta karbi bakuncin Sociedad a Copa del Rey

Gasar cin Copa del Rey

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A wasan farko Barcelona ce ta ci Sociedad daya mai ban haushi

Real Sociedad za ta ziyarci Barcelona a wasa na biyu na daf da na kusa da karshe a Copa del Rey a Camp Nou a ranar Alhamis.

A karawar farko da suka yi a gidan Sociedad, Barcelona ce ta samu nasara da ci daya mai ban haushi, kuma Neymar ne ya ci kwallon a minti na 21 a bugun fenariti.

A ranar Talata ne Deportivo Alaves ta kai wasannin daf da karshe, bayan da ta tashi wasa babu ci tsakaninta da Alcorcon a karawa ta biyu da ta karbi bakunci.

A fafatawar farko Deportivo Alves ce ta samu nasara da ci 2-0 a gidan Alcorncon, kuma Iago Aspas da Jonny ne suka ci mata kwallayen.

Barcelona wadda ke rike da kofin bara ta lashe Copa del Rey sau 28 a tarihi, sai Athletic de Bilbao mai guda 23 da kuma Real Madrid a mataki na uku da kofuna 19.