Liverpool ta yi ban kwana da League Cup

Gasar Legue Cup

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Southampton ta kai wasan karshe a gasar League Cup

Southampton ta fitar da Liverpool daga gasar League Cup ta bana, bayan da ta zura mata kwallaye 2-0 a wasanni biyu da suka fafata a karawar daf da karshe.

Southampton ta ci kwallonta tilo ne ta hannun Shane Long daf da za a tashi daga wasan a Anfield a jiya Laraba, a karawar farko ma Southampton ce ta ci daya mai ban haushi a gida.

Da wannan sakamakon Southampton ta kai wasan karshe a League Cup din, wanda rabon da ta kai irin wannan matakin a babbar gasa tun 2003.

Southampton za ta jira kungiyar da za ta kara da ita a wasan karshe a Wembley, tsakanin Hull City ko kuma Manchester United.

A karawar farko da kungiyoyin suka yi a Old Trafford, United ce ta samu nasara da ci 2-0, kuma Juan Mata da Marouane Fellaini ne suka ci mata kwallayen.