An fitar da Real Madrid daga Copa del Rey

Gasar Copa del Rey

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid ta lashe Copa del Rey sau 19 a tarihi

Real Madrid ta yi ban kwana da gasar Copa del Rey ta bana, bayan da Celta Vigo ta doke ta da ci 4-3 a karawa biyu da suka yi a wasannin daf da na kusa da na karshe.

A wasan farko da suka kara Celta ce ta ci Madrid 2-1 a Bernebeu, sannan kungiyoyin biyu suka tashi 2-2 a gidan Celta a ranar Laraba.

Celta ce ta fara cin kwallo bayan da Real ta ci gida ta hannun Danilo tun kafin a je hutu, kuma bayan da aka dawo ne daga hutun Madrid ta farke ta hannun Cristiano Ronaldo.

Daniel Wass ne ya ci Celta ta biyu kafin daga baya Lucas Vazquez ya farke wa Madrid.

A ranar Alhamis ne Barcelona wadda ta ci Real Sociedad daya mai ban haushi a wasan farko za ta karbi bakuncin Sociedad din.