China na son zuba jari a Southamptom

Southampton

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'yan wasan Southampton sun samu zuwa wasan karshe a gasar League Cup ranar Laraba bayan sun doke Liverpoolo.

Kungiyar kwallon kafar Southampton ta kwantarwa da magoya bayanta hankali kan yiwuwar saka jari da wani kamfanin China ke son yi a kulob din, yana mai cewa za a yi hakan ne don amfanin kungiyar.

Kamfanin - mai gina filayen wasa mai suna Lander Sports Development, ya ce ya cimma yarjejeniyar sayen hannun jarin daga mai kungiyar Southamton din Katharina Liebherr .

Ms Liebherr ta ce ''Hadin gwiwar da ake sa ran za a kulla din sai ya samu amincewa daga matakai da da dama yta kuma cika sharuddai masu tsauri.''

Kamfanonin China sun sayi hannayen jari daga kungiyoyin Manchester City da West Brom.

Attajirin nan na kasar Switzerland dan asalin Jamus, Markus Liebherr ne ya ceto Southamptom daga karayar jari a shekarar 2009.

'Yarsa Katharina ce ta ci gadon kungiyar bayan mutuwar Babanta a shekarar 2010 kuma ta zama shugabar kamfanin a shekarar 2014.

Southampton ce ta 11 a teburin Premier.