Roger Federer ya doke abokinsa na Switzerland, Stan Wawrinka

Federer da Wawrinka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Federer da Wawrinka abokai ne idan sun bar filin wasa

Roger Federer ya samu zuwa zagayen karshe a gasar Australian Open bayan ya doke Stan Wawrinka da 7-5 6-3 1-6 4-6 6-3.

Wannan sakamakon zai bashi damar iya lashe babbar gasar tennis ta Australia a karo na 18.

Dan wasan mai shekaru 35 a duniya zai kece raini da Rafael Nadal a ranar Lahadi mai zuwa, idan dan Sapaniyan ya doke Grigor Dimitrov a wasan dab da na karshen da za a buga a ranar juma'a.

Federer wanda ya je hutun wata shida bayan ya ji ciwo bai ci wata babbar gasa ba tun ta Wimbledon a shekarar 2012.

Shi ne mutum mafi girma wanda ya taba zuwa wasan karshe a babbar gasar tun bayan da Ken Rosewall ya yi hakan a shekarar 1974 a gasar US Open yana mai shekara 39.