Celtic ta ce mai tsaron gidanta ba na sayarwa ba ne

Gordon

Asalin hoton, .

Bayanan hoto,

Gordon na shekararsa ta uku a Celtic

Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta yi tayin sayen mai tsaron gidan Celtic, Craig Gordon.

Amma Celtic ta gaya wa jagoran teburin gasar Firimiyar cewar Craig ba na sayarwa ba ne.

Craig mai shekaru 34 kuma dan asalin Scotland na da sauran wata 18 kafin kwantiraginsa na yanzu ta kare da Celtic.

Ya koma kungiyar ne a shekarar 2014 kuma kafin nan sai da ya yi shekara biyu yana jinyar guiwa.