Rafael Nadal ya doke Grigor Dimitrov

nadal

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Nadal ya kai wasan karshe na 21 a babbar gasar tennis.

Zakaran wasan tennis, Rafael Nadal, ya samu nasarar zuwa zagayen karshe na gasar Austalian Open, inda zai fafata da abokin hamayyarsa Roger Federer.

Rafael ya samu nasarar ce bayan doke Grigor Dimitrov a karawar da suka yi a ranar Juma'a.

Dan wasan Spaniyar ya kafa tarihi ne da ci 6-3 5-7 7-6 (7-5) 6-7 (4-7) 6-4 a wasan da suka shafe tsawon sa'oi biyar suna yi, lamarin da ya kai shi ga shiga wasan karshe na babbar gasar tennis, wanda rabonsa da samun hakan tun a shekarar 2014.

Shi kuma Dimitrov zai ci gaba da jiran ranar da zai kai ga zagayen karshen bayan Nadal ya yi tarnaki a kan burinsa ta hanyar kayen da ya sha wanda shi ne irinsa na farko a wannan shekarar.

A ranar Lahadi mai zuwa ne Nadal mai shekaru 30 zai fafata da fitaccen dan wasa, Roger a Melbourne.

"Ban taba mafarkin zan sake samun kaina a zagayen karshe na gasar Australian Open ba" In ji Nadal.

Ya kara da cewa "Wani abu ne mai muhimmanci sosai a gare mu, dukkaninmu biyu mu yi wasa a babbar gasar. Na san babu daya daga cikinmu da ya yi tsammanin zai kawo wannan mataki."