Manchester City ta amsa tuhumar da aka yi mata kan kwayoyin kara kuzari

Manchester City

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Manchester City ita ce ta biyar a teburin gasar cin kofin Firimiya

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta amince da tuhumar da hukumar kwallon kafa ta Burtaniya, FA, ta yi mata game da amfani da kwayoyin kara kuzari, bayan da ta kasa bayyana inda 'yan wasanta suka shiga ba a yi musu gwaji ba.

Ana dai bukatar duka kungiyoyin kwallon kafa su bayar da bayanai na gaskiya a kan atisayen da suke yi da kuma inda 'yan wasa suke a ko da yaushe domin a samu damar yi musu gwaji.

Sai dai ana zargin City da rashin bayyana gaskiyar hakan har sau uku.

Hukumar dai na da wata doka wadda ta tanadi cin tarar duk wani kulob da ya gaza bayar da bayanan gaskiya sau uku.

An dai fahimci cewa kungiyar ba ta yi bayani game da sauye-sauyen da ta yi ba a kan horar da 'yan wasanta.