Roger Federer ya lashe gasar Australian Open

Federer

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tun 2012 rabon da Federer ya lashe gasar

Roger Federer ya yi nasarar lashe kambun gasar kwallon Tennis ta Australian Open, karo ta 18, bayan da ya lallasa abokin karawarsa Rafael Nadal a zagayen karshe na wasan.

Dan wasan mai shekara 35 dan kasar Switzerland ya lashe gasar ne da ci 6-4 3-6 6-1 3-6 6-3.

Shi kuwa Rafael Nadal ya zo na biyu bayan da ya buge Pete Sampras.

Rabon da Federer ya lashe wata babbar gasa tun a shekarar 2012 a gasar Wimbledon.

Shi ne mutum mafi girma wanda ya taba zuwa wasan karshe a babbar gasar ta Australian Open, tun bayan da Ken Rosewall ya yi hakan a shekarar 1974, a gasar US Open yana mai shekara 39.

Federer ya zamo mutum na farko a tarihi da ya yi nasarar lashe kambuna biyar ko fiye da haka a manyan gasanni uku daban-daban - biyar a Australian Open da biyar a US Open da kuma bakwai a gasar Wimbledon.