An ki sallamar wa Chelsea Gordon a karo na biyu

Craig Gordon ya ki yadda da tayin Chelsea ba
Tun farko Celtic ta ki amincewa da tayin farko da Chelsea wadda ke mataki na daya a kan teburin Premier ta yi wa Golan dan kwallon tawagar Scotland mai shekara 34.
A wata hira da BBC ta yi da kociyan Celtic, Brendan Rodgers, a ranar Lahadi ya musanta batun cewar Chelsea na zawarcin dan wasan.
Ya kuma kara da cewar "Ba ma son ya bar Celtic, kuma babu tayin da za a yi mana da zai sa mu sallamar da Golan na mu".
Gordon ya je Sunderland taka-leda daga Hearts kan kudi fam miliyan 9 a shekarar 2007, inda ya yi shekara biyar a can.
Thibaut Courtois ne ke tsare ragar Chelsea, sai dai kuma kociya Antonio Conte ya amince Asmir Begovic ya gwada sa a a wata kungiyar idan har ya samu zai maye gurbinsa a Stamford Bridge.