Crystal Palace ta sayi Patrick van Aanholt

Patrick van Aanholt

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Patrick van Aanholt ya ci kwallaye takwas was Sunderland, ciki har da kwallaye ukun da ci wa kungiyar a kakar bana

Kungiyar kwallon kafa ta Crystal Palace ta cimma yarjejeniyar sayen dan wasan Sunderland, Patrick van Aanholt, a kan kudi fam miliyan 14.

Dan asalin Netherlands Van Aanholt, mai shekara 26, ya buga wa Sunderland wasa sau 95 bayan ya koma can murza leda, a wani kwantiragin kudi fam miliyan daya da dubu dari biyar a lokacin bazarar shekarar 2014.

A yanzu Aanholt ya amice da yarjejeniyar shekara hudu da rabi, kuma jagoran kungiyar, Sam Allardyce, ya ce "Zai taimaka ta wurare biyu. Ya taimaka wajen ceto Sunderland daga fadawa rukuni na kasa a kakar bara, ba kawai a matsayin mai buga wasan baya ba, har ma ta wajen shan kwallo."

Allardyce ya kara da cewar, "Muna son ya rike mana bayan nan da kyau saboda ana cin mu kwallaye da dama."

Sunderland tana can kasa a teburin gasar Firimiya.

A wani taron manema labarai a ranar Litinin, Allardyce ya tabbatar da son sayan mai buga wa Juventus wasan baya, Martins Caceres, amma ya yi watsi da jita-jitar da ke alakantashi da son sayan dan Asernal, Carl Jenkinson.