Madrid ta ci kwallaye 51 a zagayen farko a La Liga

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Real Madrid ta ci kwallaye 51

A ranar Lahadi ne Madrid ta ci Real Sociedad kwallaye 3-0 a karawar mako na 20, bayan da Real tana da kwanta wasa daya.

A wasan farko a gasar La ligar bana, 3-0 Real ta ci Soociedad a ranar 21 ga watan Agustan 2016, kuma Gareth Bale ne ya fara ci wa Madrid kwallo a wasannin bana.

Tun daga nan 'yan wasan Madrid 17 ne suka ci mata kwallaye a wasannin La Ligar shekarar, kuma Cristiano Ronaldo ne ke kan gaba da kwallaye 13.

Sergio Ramos da kuma Álvaro Morata sun ci wa Real Madrid kwallaye shida-shida kowannensu kuma sune na biyu a yawan ci mata kwallaye a La Ligar bana.

Bayan da aka kammala zagayen farko, Real tana mataki na daya a kan teburi da maki 46, sai Barcelona da maki 42 ita ma Sevilla maki 42 ne da ita a mataki na uku.