Copa del Rey: Barcelona ta casa Atletico Madrid 2-1

Lionel Messi a lokacin da ya ci kwallonsa ta 30 a bana

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Lionel Messi ya ci kwallo 30 kenan a wasa 29 bana

Barcelona ta doke Atletico Madrid a karawarsu ta farko ta wasan kusa da na karshe na cin kofin Copa del Rey a gidan 'yan Madrid din Vicente Calderon.

Luis Suarez ne ya fara ci wa Barca kwallo a minti na bakwai da shiga fili, sannan kuma Lionel Messi ya kara ta biyu a minti na 33.

Sai dai Antoine Griezmann ya ba wa masu masaukin bakin kwarin guiwa a karo na biyu da za su yi a ranar Talata a Nou Camp, sakamakon kwallo daya da ya rama a minti na 59, wadda ya ci da kai.

Alaves da Celta Vigo su ne sauran kungiyoyin da suka kai wasan na kusa da karshe, inda za su yi wasansu na farko ranar Alhamis.