Premier Man City ta caskara West Ham 4-0

Gabriel Jesus a lokacin da yake cin kwallonsa ta farko a City

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Gabriel Jesus ya ci kwallo daya, ya kuma bayar aka ci biyu a wasanni uku da ya buga wa Manchester City

Gabriel Jesus ya ci wa Manchester City kwallonsa ta farko a wasan da suka caskara West Ham a gidanta London Stadium 4-0, a gasar Premier.

City, wadda ta bar dan wasan gabanta Sergio Aguero da mai tsaron-raga Claudio Bravo a benci, ta fara cin kwallonta ne ta hannun Kevin de Bruyne a minti 17.

Sai kuma Silva ya biyo baya da ta biyu a minti na 21, yayin da de Jesus ya kara ta uku a minti na 39, kafin Yaya Touré ya karke da ta hudu a minti na 67 da fanareti, bayan da Jose Fonte ya kayar da Sterling.

Sau biyu kenan West Ham a gidanta na shan kashi a hannun City a wannan shekara ta 2017.

A wasan da suka yi na gasar cin kofin kalubale na hukumar kwallon kafa ta Ingila FA, a watan da ya wuce, sun sha kashi 5-0.

Yanzu Manchester City da maki 46 na bayan ta hudu a teburin Premier Liverpool da bambancin kwallo 24 da 19, Kuma maki 10 tsakaninta da ta daya Chelsea mai maki 56.

West Ham tana matsayin ta goma sha daya da maki 28.