Ana nuna min bambanci - Mourinho

Mourinho ya fusata

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Mourinho ya fice daga tattaunawar da tashar talabijin ta BBC ke yi da shi a fusace

Kocin Manchester United Jose Mourinho ya ce ana nuna masa bambanci tsakaninsa da takwarorinsa na kungiyoyin Premier, bayan da suka tashi canjaras ba ci a Old Trafford da Hull City.

Kocin dan Portugal ya yi kokarin danne zuciyarsa kan yadda alkalin wasa Mike Jones ya tafiyar da wasan nasu da suka tashi 0-0 ranar Laraba a Old Trafford.

Mourinho ya nuna yadda kocin Liverpool Jurgen Klopp ya yi sa-in-sa da jami'i na hudu na bayan fili da ke taimaka wa alkalin wasa Neil Swarbrick a lokacin wasan da suka yi 1-1 da Chelsea ranar Talata.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A wasan Premier 14 ba a doke United ba, amma ta yi canjaras a wasanta uku na baya-bayan nan

Mourinho ya ce, ''idan ka duba za ka ga lalle ni ana nuna min bambanci domin idan da ni na yi fito-na-fito da jami'in da sai a dauki mataki a kaina.''

Sakamakon wasan ya sa Manchester United ta ci gaba da zama a matsayi na shida da maki 42, a wasan na mako na 23.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Golan Hull City Eldin Jakupovic ya kare hare-hare da yawa da 'yan Manchester United suka kai

Ita kuwa Hull City da dago zuwa ta 19 da maki 17, inda take neman tsira daga faduwa daga gasar ta Premier.

A bana an hukunta Mourinho sau biyu da hana shi zuwa bakin fili bisa sukan mataimakin alkalin wasa Taylor, kafin zuwan kungiyarsa gidan Liverpool a watan Oktoba.

Da kuma laifin kwallo da ya yi da robar ruwa a fusace a lokacin da suka yi canjaras a Old Trafford da West Ham a watan Nuwamba, inda dukkanin laifukan sun saba wa dokokin hukumar kwallon kafa ta Ingila.

Shi ma kocin Arsenal Arsene Wenger, a yanzu haka yana cikin haramcin halartar wasa hudu bayan da aka same shi da laifin zagin mai taimaka wa alkalin wasa na hudu Anthony Taylor, a lokacin wasan kungiyarsa a gida da Burnley a watan da ya wuce.