Ban damu da makomar Saido Berahino ba — Pulis

Saido Berahino

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Saido Berahino ya maye gulbin a gasa tsakanin su da Everton a ranar Laraba

Kocin West Brom Tony Pulis ya ce bai damu da makomar Saido Berahino ba saboda dan wasan gaba na Stoke City din ba ya gabansa.

Kocin Stoke City Mark Hughes, ya tabbatar da cewa an dakatar da Berahino wanda ya koma kungiyarsa a watan Janairu, na tsawon makonni takwas a lokacin da yake West Brom.

Koci Pulis ya yi wannan kalamai ne bayan da jaridu suka ruwaito cewa an dakatar da shi ne bayan gwajin shan kwayoyi da aka yi masa ya nuna yana tu'ammali da kwayoyin.

"Duk wani abu da kungiyar Stoke ta tambaya a game da shi sai da muka gaya musu gaskiya," inji Mista Pulis da yake shaida wa BBC.

Ya ce, "Mun ki sake daukarsa ne saboda lafiyar jiki da kwakwalwarsa ba su kai yada muke bukata ba."

"Wannan kungiyar ta matukar taimakawa Brahino. Yadda muka dinga bashi kariya, da kulawa da shi. Kamata ya yi ma ya gode mana sosai." Inji Pulis.

Dan wasan mai shekara 23 zai koma wasa da Stoke City ne a gasar Premier ranar Asabar.

Da aka tambaye shi ko a yanzu Hughes ne mutumin da zai taimakawa Berahino, sai Mista Pulis ya ce, "Ni a yanzu ba abin da ya dame ni da lamarin Berahino."

Ya kara da cewa, "Shekarata biyu a wannan kungiyar, kuma ba shi ne matsalata ba. Ina masa fatan alheri."

Hukumar yaki da amfani da kwayoyin kara kuzari a wassani ta duniya ce dai ta dakatar da Saido Berahino don ladabtarwa.