Frank Lampard ya yi ritaya daga buga tamaula

Frank Lampard

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Frank Lampard ya shafe shekara 21 yana buga tamaula

Tsohon dan wasan gaba na Chelsea da Ingila Frank Lampard ya yi ritaya daga buga tamaula bayan shekara 21.

Dan wasan mai sheakara 38, wanda ya shafe shekarar da ta gabata yana wasa a babbar kungiyar kwallon kafa ta Amurka, da ke birnin New York.

Lampard ya sanar da matakin yin ritayar ne a kafefen sada zumunta na zamani a ranar Alhamis.

"Duk da cewa na samu gayyata daga kungiyoyi daban-daban, amma ina ganin tun da na kai shekara 38 kamata ya yi na yi ritaya, don na fuskancin sabon babin rayuwata ta gaba kuma," inji Lampard.

Ya kara da cewa, "ina mika godiyata ga kungiyar kwallon kafa saboda damar da ta bani don na yi karatun kwarewa a aikin koci, kuma zan yi kokarin ganin na yi amfani da damar samun aiki a wannan bangare."

Lampard dai ya samu nasarar cin manyan kofuna da suka hada da na gasar Premier uku da kuma na gasar kofin zakarun Turai a shekarar 2012.

Ya kuma ci kofuna hudu na gasar kalubale da na gasar Lig-lig ta Turai da kuma na gasar Europa.