Arsenal: Aaron Ramsey ba zai yi wasa ba na mako uku

Aaron Ramsey

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Aaron Ramsey ba zai yi wasa ba har mako uku

Kociyan Arsenal Arsene Wenger, ya ce dan wasan tsakiya Aaron Ramsey, ba zai buga wasanni ba har tsawon makwanni uku, sakamakon rauni da ya samu a gwiwar kafarsa.

Ramsey dai ya bar fili yana dingishi a karawarsu da Watford a tsakiyar mako.

Wenger ya ce, "Yanzu dai za mu rashin Aaron Ramsey, kuma muna ganin zai kai kwanaki 21 bai buga wasa ba."

Ya kara da cewa, "Mun dan samu gurbi a tawagarmu yanzu, amma muna da 'yan wasa masu tasowa da muke da kyakkyawan fata a kansu."

Amma kuma tun da farko dai kafin wasannin Stamford Bridge, Wenger ya musanta cewa suna da-na-sanin bayar da aron dan wasan tsakiyarsu Jack Wilshire ga Bournemouth na tsawon kakar wasanni guda.