Da wuya Leicester ba ta fadi daga Premier ba - Schmeichel

Golan Leicester Kasper Schmeichel, ya ce dole sai sun zage damtse

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Leicester ce kadai a kungiyoyi hudu na gaba a dukkanin gasar Ingila da ba ta ci kwallo ba a gasarta a 2017

Mai tsaron ragar zakarun Premier Leicester City, Kasper Schmeichel, ya ce wasannin da suke yi na kare kofin abin kunya ne, kuma in ba su tashi tsaye ba za su fadi daga gasar.

Golan ya ce karshenta kungiyar ta fadi daga gasar Premier, muddin suka ci gaba da irin abin kunyar da suke yi na wasa.

Maki daya ne kacal, tsakanin zakarun na Premier tsakninsu da rukunin faduwa daga gasar, bayan da Manchester United ta bi su har gida ta kunyata su da ci 3-0.

Har yanzu kungiyar ba ta ci ko da wasa daya ba na Premier a wannan shekara ta 2017, kuma ba ta jefa ko kwallo daya ba a raga a wasannin gasar biyar da ta yi na karshe.

Schmeichel ya bayyana cewa abin yana damun dukkanin 'yan wasan, domin ba abu ne mai dadi ba.

Ya kar da cewa dole ne kowa ne dan wasa ya tashi tsaye, ya bayar da gudummawarsa, in ba haka ba kuwa, za su fice daga gasar.

A bara a daidai irin wannan lokaci Leicester ce ta yi nasara a karawar da ta yi da Manchester City 3-1 a Etihad.

Nasarar da ta ba ta damar tazara da maki biyar a saman tebur, kuma hakan ya sa ta kama hanyar daukar kofin, abin da ba a yi tsammani ba.

A yanzu dai tazarar maki 38 ne tsakanin Leicester da ja-gaba a tebur Chelsea.

Kuma wasu rahotanni na cewa kocin kungiyar Claudio Ranieri ya rasa goyon bayan 'yan wasansa.

To amma Schemeichel bai ce komai ba a kan wannan jita-jita, sai dai shi kocin ya ce 'yan wasansa na tre da shi.