Fabianski: Dole Swansea ta koyi darasi

Lokacin da Gabriel Jesus ya ci Golan Swansea Lukasz Fabianski, kwallon Man City ta biyu

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Golan Swansea Lukasz Fabianski, ya ce ya kamata a ce ya yi kokari sosai na hana kwallon da Gabriel Jesus ya ci su dab da tashi

Mai tsaron ragar Swansea City Lukasz Fabianski, yana ganin kungiyar na taka rawar-gani duk da rashin nasarar da ta yi a gidan Manchester City, amma kuma sai ta koyi darasi daga wasan.

Swansea ta gamu da cikas a karawar, sakamakon kwallo ta biyu da Gabriel Jesus ya ci wa masu masaukin bakin ana dab da tashi, wadda ta sa City ta kwashi maki ukun gaba daya.

Duk da cewa maki daya ne tsakanin kungiyar da rukunin masu faduwa daga gasar Premier, Fabianksiwas na ganin kungiyar tasu na cigaba.

Ya ce wasan da suka yi da Manchester Cityn ya ci ya ba su kwarin guiwa, idan aka duba matsayin City din, da kuma cewa a gidanta ne aka yi wasan.

Golan ya ce da sun yi sa'a kuma a ce ya yi kokari fiye da yadda ya yi a wasan, da sun samu maki daya a karawar.

Dan wasan na Poland yace ko ba komai, wasan da suka yi ya nuna cewa sun yi gyara a bayansu, kuma za su dora a kan hakan.

A wasanta na gaba wanda a gida za ta yi, za ta kara ne da masu rike da kofin gasar ta Premier Leicester City, a ranar Lahadi.

Dukkanin kungiyoyin biyu suna da yawan maki daya ne 21, amma Leicester na gaba da yawan bambancin kwallo.