Boksin: Za a rika amfani da na'urar daukar hoton kwakwalwa

Na'urar gano jini a kwakwalwa

Asalin hoton, Others

Bayanan hoto,

Cikin minti uku na'urar za ta kammala nazari tare da gano inda jini ya zuba a kwakwalwa

Za a rika amfani da wata karamar na'ura ta hannu, ta daukar hoton kwakwalwa domin kula da lafiyar 'yan damben boksin a lokacin wasan.

Hukumar damben boksin ta Birtaniya da Ireland (BIBA), na sa ran fara amfani da na'urar a wata gasa da za a yi ta damben a Bradford, ranar 26 ga watan Fabrairu.

A watan Satumba Mike Towell ya mutu sakamakon raunin da ya ji a ka, a wani dambe da suka yi, wata shida bayan an kwantar da Nick Blackwell, a asibiti saboda jinin da ya taru a kwakwalwarsa a wani boksin da suka yi.

Shi dai Towell ya kasance yana fama da ciwon kai 'yan kwanaki kafin damben, wanda ya yi sanadin mutuwarsa, bayan da Dale Evans ya doke shi a turmi na biyar.