An hukunta dan wasa saboda buga wa alkalin wasa kwallo a ido

Alkalin wasa Gabas, dan Faransa ya rufe fuskarsa
Bayanan hoto,

Alkalin wasa Gabas bayan da Shapovalov ya doka masa kwallo a fuska

An ci tarar dan wasan tennis Denis Shapovalov na Canada dala dubu bakwai bayan da aka same shi da laifin buga wa alkalin wasa kwallo a fuska a fafatawarsa da Kyle Edmund na Birtaniya a gasar Davis Cup.

Edmund na gaban dan wasan na Canada mai shekara 17 a lokacin wasan da ci 6-3 6-4 2-1, lokacin da cikin fushi ya doka kwallon waje, bisa tsautsayi sai ta samu alkalin wasa Arnaud Gabas a ido.

Hukumar gasar ta ci tarar dan wasan na Canada dala dubu biyu kan buga kwallon waje da kuma tarar dubu biyar ta dabi'ar da ba ta dace da wasa ba.

A ka'ida ya kamata a ci shi tarar dala dubu goma ne, amma kasncewar ba da gangan ya buga wa alkalin wasan kwallon ba, aka rage tarar.

Bayanan hoto,

Denis Shapovalov lokacin da yake buga kwallon

Duk da haka dai hukumar kwallon tennis ta duniya za ta iya kara daukar mataki a kai.

Sakamakon abin da dan wasan na Canada ya yi, yanzu an fitar da kasar daga gasar wadda ake yi a Ottawa ta Canadan.

Daga baya ya ba wa alkalin wasan hakuri tare da neman gafararsa, kafin alkalin wasan ya tafi asibiti domin a duba lafiyarsa kan tambarin da kwalon ta masa a fuska da kuma kumbura masa ido.