Har yanzu ban yi jimamin rashin matata ba yadda ya kamata -Ferdinand

Rio Ferdinad

Asalin hoton, Ferdinand

Bayanan hoto,

Ferdinand ya ce, ya rasa Rebecca a matsayin mata da 'yar uwa da kanwa da 'ya da kuma jika

Tsohon dan wasan Manchester United da kuma Ingila Rio Ferdinand, ya ce har yanzu bai samu cikakken lokacin da zai yi jimamin mutuwar matarsa Rebecca ba.

Matar tsohon dan wasan wdda suka haifi 'ya'ya uku, ta rasu ne sakamakon cutar daji ta mama a shekarar 2015, lokacin tana da shekara 34.

Ferdinand ya bayyana hakan ne a wani shirin talabijin na BBC wanda aka shirya don jin ta bakin iyayen da suka rasa matansu, kan yadda suka ji radadi da jimamin mutuwar, wanda za a nuna a lokacin damuna.

Tsohon kyaftin din na Ingila, ya yi wa kasarsa wasa 81, kuma ya shafe shekara 12 a kungiyar Manchester United.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Ferdinand da Rebecca sun haifi 'ya'ya uku

Ferdinand da Rebecca sun kasance tare tsawon shekaru da dama kafin su yi aure a 2009, kuma sun haifi 'ya'ya uku.

'Yan makonni bayan mutuwar matar tasa ne, Rio Ferdinand ya yi ritaya daga wasan kwallon kafa, inda ya yi wa kungiyarsa ta karshe QPR, wasan karshe a watan Maris na wannan shekara.