An haramta wa 'yan wasa sauya kasa

Wasu 'yan wasan Kenya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan wasan Kenya da dama sun wakilici wasu kasashen a gasar Olympics ta Rio

Hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya, IAAF, ta haramta wa 'yan wasa sauya kasashensu daga yanzu, ganin yadda 'yan Afirka ke komawa wasu kasashe.

Shugaban hukumar Lord Coe, ya ce yawan yadda ake samun 'yan wasa na sauya kasarsu fiye da sau daya, musamman ma daga Afirka, hakan ya nuna cewa dokokin da ake da su ba su da sauran amfani.

'yan wasan Kenya sama da ashirin ne suka wakilci wasu kasashe a gasar wasannin Olympics da aka yi a birnin Rio na Brazil a shekarar da ta wuce.

Haka kuma, 'yan wasan tseren dogon zango da yawa daga kasar Habasha su ma sun sauya kasarsu.

Wakilin Afirka a hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsallen ta duniya (IAAF Council), Hamad Malboub, ya ce yanzu 'yan wasan Afirka na tururuwr komawa duk kasar da za ta iya biyansu kudi mai yawa.