Djibril Cisse ya bar kwallon kafa ya koma harkar kida da waka

Djibril Cisse

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Bayan Liverpool Djibril Cisse wanda ya yi wa Faransa wasa 41, ya yi kungiyoyi da dama

Tsohon dan wasan Liverpool da kuma Faransa Djibril Cisse ya yi ritaya daga buga wasan kwallon kafa yana da shekara 35, ya koma harkar kade-kade da wake-wake.

A da Cisse ya dakata ne da wasan na kwallon kafa a watan Oktoba na shekara ta 2015 saboda ciwon kugu, da nufin dawowa idan an yi masa tiyata a shekarar da ta wuce.

Ya yi atisaye da kungiyarsa ta farko Auxerre, domin ya murmure, amma sabod bai samu kungiyar da ta dauke shi ba, sai ya yanke shawarar yin ritaya bayan shekara 17.

Yanzu dai Cisse zai mayar da hankali ne kan sana'ar kade-kade da wake-wake, a matsayin mai sanya wakoki da hada su da kuma mai fashin-baki.

Dan wasan ya ce, :"In matukar kaunar kasancewa da wasan kwallon kafa har yanzu, wanna ita ce rayuwa ta gaba daya.''

"Na so a ce na ci gaba da sana'ata ta wasan kwallon kafa, amma kuma abin takaicin a yanzu na kawo karshen sana'ar."

Cisse, wanda ya yi wa Faransa wasa 41, ya yi Liverpool tsawon shekara uku tun daga 2004, kafin ya koma kungiyar Marseille ta Faransa.

Dan wasan ya kuma yi kungiyoyin Sunderland da Panathinaikos da Lazio da QPR da Kuban Krasnodar d kuma Bastia.