Leicester ta ba wa Ranieri goyon baya duk da rashin kokarinsa

Claudio Ranieri

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Leicester ba ta ci wasa ko daya ba a waje a wannan kakar

Leicester City ta ba wa kocinta Claudio Ranieri cikakken goyon baya duk da cewa maki daya ne tsakanin Zakarun Premier da matakin faduwa daga gasar.

Kocin dan Italiya na cikin matsin-lamba kasancewar wasa biyu kawai ya ci a wasanni goma sha biyar na Premier da kungiyar ta yi na karshe

Sai dai a sanarwar da ta fitar kungiyar ta ce, baki dayanta tana goyon bayan , kuma za ta ci gaba da goyon bayan kokocinta.

Kocin ya ce, wannan ba wata matsala ba ce, abu ne da aka saba , idan ba ka nasara a wasanka, ka rasa kwarin guiwa da goyon baya.

Wasu magoya bayan kungiyar na hankoron ganin an sauya kocin, kasancewar kungiyar ita ce ta 16 a tebur kuma har yanzu ba ta ci ko wasa daya ba a wannan shekara ta 2017.

Bayan wasan da Manchester United ta doke su a gida mai tsaron ragar kungiyar Kasper Schmeichel ya bayyana wasanninsu na kare kofin da cewa abin kunya ne, kuma da wuya idan ba su fadi daga Premier ba.

Ita kanta kungiyar ta ce lalle ne a samu sauyi kan yadda take wasa a yanzu, amma ta ce ya kamata a ba wa Ranieri damar kawo sauyin.