Southampton na dab da daukar Caceres

Martin Caceres a wasan Uruguay da Ingila na cin kofin duniya na 2014

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Martin Caceres na cikin tawagar Uruguay da ta doke Ingila a gasar cin kofin duniya na 2014

Southampton na dab da kammala yarjejeniyar daukar tsohon dan wasan baya na Barcelona da Juventus Martin Caceres, sabod rshin wasu 'yan wasanta na baya.

Dan wasan dan kasar Uruguay, mai shekara 29, zai dawowa kungiyar ta Premier da zarar an kammala ba shi takardar izinin aiki da kuma wasu ka'idoji.

Caceres, wanda ya buga wa kasarsa Uruguay wasa sau 68 ya bar Juventus ne a lokacin kasuwar saye da sayar da 'yan wasa ta bazara, bayan da kwantiraginsa ya kare da kungiyar.

Southampton za ta sayo Caceres ne domin maye gurbin Virgil van Dijk wanda zai yi jinyar wata uku, ta ciwon da ya ji a wuyan kafarsa.

Da kuma kasancewar dan wasanta Jose Fonte, ya koma kungiyar West Ham.

Ya kuma yi wa zakarun Italiyar wasa 77, sannan ya yi kungiyar Barcelona da Sevilla a gasar La Liga ta Spaniya.

Rabon da Caceres ya buga wani wasa na wata gasa tun watan Fabrairu, bayan da ya ji rauni a cinya.