'Dole ne koci-kocin Rasha masu amfani da abubuwan kara kuzari su bar aiki'

Mataimakin Fira Ministan Rasha Vitaly Mutkon

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mutko, wanda ya kama aiki a Oktoba, yana ta magana tun lokacin da aka zargi hukumomin Rasha da hannu a amfani da abubuwan kara kuzari kan 'yan wasanta

Mataimakin Fira Ministan Rasha Vitaly Mutko, ya ce dole ne masu horar da 'yan wasan kasar wadanda ba su san yadda za su aiki ba tare da amfani da abubuwan kara kuzari ba su bar aiki.

A watan Nuwamba na 2015, hukumar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya ta dakatar da Rasha a kan samun hukumomin kasar da hannu a cogen amfani da abubuwan kara kuzari da 'yan wasan kasar suka yi.

Kuma a ranar Litinin hukumar ta IAAF, ta tsawaita dakatarwar har zuwa lokacin gasar wasannin duniya ta 2017, abin da ke nufin kasar ba za ta dawo fagen wasannin ba har sai watan Nuwamba.

Yanzu dai Rasha ba za ta shiga gasar ta duniya ba, wadda za a fara ranar 4 ga watan Agusta a Landan.

Amma wasu daga cikin daidaikun 'yan wasan kasar da suka gabatar da shedar gwajin amfani da abubuwan kara kuzari na wata hukuma mai zaman kanta za su iya samun damar shiga gasar, amma kuma ba da sunan kowace kasa ba.

Kuawo yanzu hukumar wasannin ta duniya na duba takardun 'yan wasa 35 daga Rashar wadanda suka gabatar da takardunsu na shedar wanke su daga amfani da abubuwan kara kuzari na wasu hukumomin masu zaman kansu.