Copa del Rey: Neymar ba zai yi wasa ba

Neymar da Suarez da Pique

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Barcelona ce ke rike da Copa del Rey, bayan doke Sevilla a wasan karshe a bara

Barcelona za ta yi wasanta na karawa ta biyu ta wasan kusa da karshe ta kofin Copa del Rey da Atletico Madrid a Nou Camp, ba tare da Neymar ba.

Barca ta yi nasara a karawar farko da suka yi a gidan Atletico, Vicente Calderon, da ci 2-1, inda aka ba wa dan wasan na Brazil katin gargadi na uku a gasar.

Shi ma dan wasan tsakiya na Atletico Madrid din Gabi ba zai yi wasan na Talata ba, saboda hukunci.

Kocin Barcelona Luis Enrique ya ce, suna bukatar su yi nasara a wasan, su ci akalla kwallo biyu, saboda haka za su sa ran ganin yadda Atletico za ta yi kasada, saboda 'yan wasansa, ya ce, kwararru ne a babban wasa.

Dan wasan baya na Barcelona Gerard Pique ya samu sauki, kuma zai buga wasan, bayan da ya ji rauni a wasan da suka ci Athletic Bilbao 3-0, a karshen mako.

Ana kyautata ganin duk kungiyar da ta yi nasara tsakanin Barca da Atletico a wasan, ita za ta iya daukar kofin na King's Cup.

Kungiyar da ta yi nasarar za ta hadu da tsakanin Alaves ko Celta Vigo, wadanda su kuma za su yi karawarsu ta biyu ta wasan kusa da karshen ranar Laraba