Ritayar Lahm ta shammace mu- Bayern

Phillip Lahm a tawagar Bayern Munich

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Lahm ya yi wa Bayern Munich wasa 501

Bayern Munich ta ce ta yi matukar mamaki da sanarwar ritayar kyaftin dinta Philipp Lahm daga wasan kwallon kafa, a karshen kakar bana.

Lahm mai shekara 33, ya shiga kungiyar tun yana shekara 11, kuma kusan ya shafe rayuwarsa ta kwallon kafa gaba daya a kungiyar, inda zai yi ritaya a karshen kakar bana.

Tsohon kyaftin din na Jamus, wanda ya dauki kofin duniya na 2014, yana da kwantiragi da kungiyar tasa har zuwa 2019.

Bayanan hoto,

Philipp Lahm ne ya ci kwallon farko ta gasar cin kofin duniya na 2006

Kuma ya ki amincewa da tayin karbar mukamin darektan wasanni na kungiyar da aka yi masa, idan ya yi ritayar.

Shugaban kungiyar ta Bayern Munich Karl Heinz Rummenigge, wanda ya ce kungiyar ta yi matukar mamaki da sanarwar daga dan wasan da wakilinsa, ya ce kofarsu za ta ci gaba da kasancewa a bude ga Lahm.

A shekara ta 2002 ne Lahm ya fara buga wa Bayern wasa, kuma duk tsawon wannan lokaci ya kasance da kungiyar in banda kaka biyu da ya tafi aro a Stuttgart tsakanin 2003 da 2005.

Lahm ya dauki kofin gasar Jamus ta Bundesliga 7, da kofin kalubale na kasar 6, da na Zakarun Turai, sannan kuma ya jagoranci tawagar (kyaftin) Jamus a gasar kofin duniya ta 2014.

Lahm wanda ya kasance daya daga cikin 'yan wasan Jamus da suka samu nasara a sana'ar wasan kwallon kafa, ya sanar da aniyarsa ta yin ritaya a karshen kakar bana, bayan wasansa na 501, na kofin Jamus, ranar Talata, wanda Bayern ta ci Wolfsburg 1-0.