Na rude bayan da na buga wa alkalin wasa kwallo

Shapovalov a lokacin da yake nadama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shapovalov ya ce har abada ba zai kara yadda ya aikata irin wannan abu ba

Dan wasan tennis na Canada Denis Shapovalov ya ce da alkalin wasan da ya buga wa kwallo a fuska ya ji rauni sosai, da bai san yadda zai ji ba a rayuwarsa, domin shi kansa ya rude da abin ya faru.

Dan wasan Birtaniya Kyle Edmund yana gaban Shapovalov da ci 6-3 6-4 2-1, a gasar kofin Davis, inda cikin fushi ya buga kwallon waje, ta samu alkalin wasa Arnaud Gabas a ido.

Shapovalov ya ce ya san illar kwallo idan ta doki mutum, babban abin da ya damu da shi a lokacin shi ne a ce dai alkalin wasan bai jikkata ba.

Asalin hoton, others

Bayanan hoto,

Alkalin wasa Gabas bayan da Shapovalov ya doka masa kwallo a fuska

Ya kara da cewa shi kansa ya rude, bai ma san halin da yake ciki ba har tsawon kusan minti goma, abin da zai iya tunawa kawai shi ne ya je ya zauna, yana tambaya ko alkalin wasan ya ji rauni.

An rangwanta wa dan wasan mai shekara 17 tarar da ya kamata a ci shi, zuwa dala dubu bakwai saboda ba da niyya ya aikata laifin ba.

Birtaniya ce ta yi nasara a gasar ta zagayen farko a Ottawa da ci 3-2, wanda hakan ya sa za ta je wa Faransa wasan dab da na kusa da karshe a watan Afrilu