Kofin FA: Leicester na fatan nasara a kan Derby

Darren Bent na murnar kwallon da ya rama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Darren Bent ya rama kwallon da ya ci gidansu (Derby) a karawarsu ta farko da Leicester

Kocin Leicester Claudio Ranieri ya ce zai yi sauye-sauye a wasan da kungiyarsa za ta maimaita na zagaye na hudu, na cin kofin kalubale na FA, da kungiyar Derby ranar Larabar nan.

Sabon dan wasansa Molla Wague ba zai buga ba wasan ba, wanda za a fara da karfe 8:30 agogon Najeriya, saboda ba ya kungiyar lokacin da aka yi wasan farko.

Sannan kuma Islam Slimani da Leonardo Ulloa har yanzu ba su warke ba daga raunin da suke jinya.

Dan wasan gaba na Derby David Nugent, ya dawo atisaye, kuma kila ya buga wasan da tsohuwar kungiyarsa.

Cyrus Christie da Nick Blackman da kuma Max Lowe, dukkaninsu 'yan wasan Derby, su ma sun dawo.

Yayin da George Thorne da Craig Forsyth da Will Hughes su kuwa har yanzu suna jinya.

Wannan wasan nasu shi ne kadai na cin kofin FA na zagaye na hudu da aka taba tashi canjaras.

A wasan na farko da suka yi a watan da ya wuce a gidan County sun tashi ne 2-2.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ranieri na yi wa Mahrez bayani

Leicester wadda take fama a gasar Premier inda take matsayi na 16 da maki 21 a wasa 24, tana fatan nasara a fafatawar da Derby za ta kawo mata karshen halin da take ciki.

A tarihin kungiyoyin biyu Leicester ta doke Derby a haduwarsu goma a duk wata gasa da suka taba fafatawa.

A duk tsawon wannan lokaci lokacin ta County ta taba yin nasara a kan Leicester shi ne a gida a watan Maris na 2013 da ci biyu 2-1 bisa jagorancin koci Nigel Clough.