Barcelona za ta kalubalanci korar Suarez

Luis Suarez lokacin da alkalin wasa ya kore shi

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Tun da farko Luis Suarez ya ci wa Barca kwallon da ta ba ta damar zuwa wasan karshe, da za ta yi tsakanin Celta Vigo ko Alaves

Barcelona za ta kalubalanci katin korar da aka ba wa dan wasanta na gaba Luis Suarez, wanda zai hana shi wasan karshe na cin kofin Copa del Rey.

Sau biyu alkalin wasa ya ba wa Suarez katin gargadi a wasan da suka yi na biyu na wasan kusa da karshe,ranar Talata wanda suka tashi 1-1 da Atletico Madrid.

Kati na biyu da aka ba shi saboda ya kama kan koke, shi ne kungiyar za ta daukaka kara a kai.

Kungiyar za ta kuma daukaka kara a kan katin gargadin da aka ba wa Sergio Busquets, lokacin da ya buga kwallo waje, sa'ilin da aka samu kwallo biyu a filin.

Sai dai shi Busquets zai iya yin wasan karshen ko da Barcelonan ba ta yi nasara ba a daukaka karar da za ta yi a kansa.

Barca ta gama wasan ne da mutane tara, saboda kafin korar Suarez, alkalin wasa ya sallami Sergi Roberto tun da farko saboda kati biyu na gargadi da aka ba shi.

Kungiyar ta kuma gamu da wata matsalar domin dan bayanta Javier Mascherano ya ji rauni a cinyarsa a wasan, kuma ba a san lokacin da zai warke ba kawo yanzu.