Kofin Duniya: Qatar na kashe dala miliyan 500 duk mako

Wani daga cikin aikin sabbin filin wasan da ake ginawa a Qatar

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Qatar na sa ran gama kashi 2 bisa 3 na ayyukan gasar kofin duniyar na 2022 a wata 24

Qatar na kashe dala miliyan 500 duk sati wajen gina muhimman abubuwan da ake bukata na gasar cin kofin duniya da za ta karbi bakunci a shekarar 2022.

Ministan kudi na kasar, Ali al-Emadi wanda ya fadi hakan, ya ce suna sa ran ci gaba da kashe wannan kudin duk mako, har tsawon shekara 3 zuwa 4, wajen gina sabbin filayen wasa, da tituna da layin-dogo da asibitoci.

Kasar mai arzikin iskar gas na sa ran kashe sama da dala biliyan 200 a aikin gaba daya.

Sai dai ministan ya musanta maganar cewa gasar cin kofin duniyar na 2022 za ta kasance wadda tafi kowacce a tarihi cin kudi.

Gasar cin kofin duniya na 2014 da aka yi a Brazil kamar yadda aka ce ta lashe dala biliyan 11, yayin da Rasha kuma ta kara yawan kudaden da za ta kashe don shirya wa gasar kofin duniya na 2018 daga dala miliyan 321 zuwa biliyan 10.7.

A ranar Talata ministan kudin na Qatar, ya sheda wa manema labarai a birnin Doha cewa tuni sun bayar da kashi 90 cikin dari na kwangilar ayyukan, kuma za a kammala kashi biyu bisa uku, nan da wata 24.

Domin cimma wannan buri, kamfanoni sun dauko ma'aikata 'yan kasashen waje, galibi daga kasashen Kudancin Asia, wadanda kungiyoyin kare hakkin dan adam suka ce ana ci da guminsu, tare da sa su aiki a yanayi mai hadarin gaske.

Gwamnatin Qatar din ta musanta wannan zargi, kuma a watan Disamba ta yi wasu sauy-sauye na kyautata 'yancin ma'aikata 'yan kasashen waje.

Sakamakon tashin farashin mai a duniya, yanzu kasar tana samun karin kudade, abin da ya sa, ake samun sassauci kan matakan tsuke bakin aljihu na gwamnatin kasar.

Amma daman ministan kudin na Qatar ya ce matsalar karancin kudi ba za ta shafi kason da aka ware wa aikin ba